An ƙara samun fashewar wani bututu a Ribas

Spread the love

Wani bututu ya sake fashewa a wata cibiyar mai a Soku, ƙaramar hukumar Akuku Toru a Jihar Ribas, makonni ɗaya kacal bayan fashewar bututun Trans Niger Pipeline a yankin Bodo, ƙaramar hukumar Gokana. Ƙungiyar Youths and Environmental Advocacy Centre (YEAC-Nigeria) ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce fashewar ta faru ne da sanyin safiyar Lahadi.

Sanarwar ta bayyana cewa fashewar ta yi sanadiyar gobara, wanda taa riƙa hura wuta sama da hayaki mai yawa. Duk da cewa ba a tabbatar da musabbabin fashewar ba, akwai raɗe-raɗin cewa zai iya zama tangarɗan kayan aiki, ko hari na maƙiya. Wannan shi ne karo na uku da ake samun irin wannan fashewar a wuraren mai a Jihar Ribas cikin mako guda, lamarin da ke ƙara tayar da hankulan jama’a.

A yayin da ake ci gaba da fuskantar waɗannan matsalolin tsaro, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, mataimakinsa da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar, bisa zargin gazawa wajen kare muhimman gine-ginen mai a jihar. Wannan mataki ya biyo bayan wani bidiyo da ya bazu, inda wasu matasa suka yi barazanar tsige gwamnan daga muƙamin sa.

Kungiyar YEAC-Nigeria ta yi kira da a gudanar da bincike mai zurfi kan wannan sabon lamarin tare da buƙatar hukumar NOSDRA ta gudanar da ziyarar bincike tare da sauran masu ruwa da tsaki domin gano musabbabin lamarin. Haka kuma, Ƙungiyar ta buƙaci a hukunta duk wanda aka samu da hannu wajen aikata wannan aika-aika, domin tabbatar da bin dokokin da ke ƙunshe cikin dokar masana’antar man fetur (PIA) ta shekarar 2021.

By ukarofi