‘Yan bindiga sun farmaki masallata da kashe mutane 44 a Nijar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Lamarin ya auku ne a ranar Juma’a yayin da masallatan suke tsaka da sallar juma’a a ƙauyen Fombita na yankin Kokorou, wanda kusa ya ke da iyakar ƙasashe Nijar, Burkina Faso da Mali, kuma cibiyar masu ikirarin jihadi a Yammacin Afrika da ke alaƙanta kansu da Al-ƙa’ida.

Ma’aikatar Tsaro ta Nijar ta ɗora alhakin harin akan ƙungiyar EIGS da ake jingina ta ga ƙasar musulunci, kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa, ranar Juma’a.

Bayan harin masallatan ne sai maharan kuma suka cinna wuta a wata kasuwa da wasu gidaje a yankin.

Sanarwar ta ƙara da cewa, dakarun tsaro sun tabbatar da mutuwar mutane 44 da wasu 13 da samu munanan raunuka.

Da haka ne aka ware kwanaki uku na jimamin waɗanda abin ya shafa a ƙasar.

By Babaji