
Daga BELLO A. BABAJI
Babbar Kotun Tarayya dake Lokoja a Jihar Kogi, ta yi hukuncin haramta wa Hukumar Zaɓe (INEC) karɓar yin kiranye da al’ummar mazaɓar jihar ta Tsakiya suka yi akan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Kotun, wadda ta yi hukuncin a ranar Juma’a, ta tabbatar da cewa yin kiranyen abu ne da doka ta amince da shi kuma al’umma suna da damar su yi hakan.
Ta kuma yi kira ga al’ummar mazaɓar da su gudanar da abinda doka ta sahale masu cikin kwanciyar hankali da lumana.
Lamarin ya biyo bayan hukuncin Kotun ne na hana INEC da jami’anta karɓa ko yin hukunci akan duk wani ƙorafi da mambobin mazaɓar suka sanya wa hannu.
Haka kuma Kotun ta yi wa INEC da jami’anta iyaka kan yin hukunci akan ƙorafe-ƙorafen da aka samu da ke ɗauke da sanya hannu na bogi da kuma yin zaɓe akan su.
An dage sauraron ƙarar zuwa ranar 6 ga watan Mayu, 2025.
