X: NFF ta sanar da shafin bogi da aka buɗe da sunan kocin Super Eagles, Eric Chelles

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Ƙasa, NFF, ta ankarar da al’umma game da shafin bogi da aka buɗe a kafar X da sunan kocin Super Eagles, Éric Chelle.

A sanarwar da fitar ta kafar, NFF ta ce Chelle bai da wani shafi a kafar, inda ta yi gargaɗin cewa kada a jingina masa abinda aka gani a can, wanda ƴan damfara ne suka buɗe shi.

Ta ce shafinsa guda ɗaya ne, wanda shi ne a [@eric_chelle] a kafar Instagram.

Don haka ta yi kira ga al’umma da su riƙa amfani da shi wajen ɗaukar labaran da suka shafi kocin kai-tsaye.

By Babaji