Ribas: Gwamnonin PDP sun maka Tinubu da Majalisar Dokoki a Kotun Ƙoli

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnonin da ke ƙarƙarshin jam’iyyar PDP sun shirya shigar da Shugaba Bola Tinubu da Majalisar Dokoki ƙara a Kotun Ƙoli bisa sanya dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas.

A ranar 18 ga watan Maris ne Shugaba Tinubu ya sanya dokar, inda ya ce ya yi hakan ne la’akari da rikicin siyasa da ya ta’azzara gami da lalata tashoshin mai da ake yawan yi a jihar.

Tinubu ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa da kuma Majalisar dokokin jihar, inda ya naɗa Ibok-Ete Ibas a matsayin mai jagorantar harkokin shugabanci a jihar.

A ranar Laraba ne gwamnonin Jam’iyyar PDP suka lashi takobin ƙalubalantar hukuncin a kotu.

Gwamnonin da za su shigar da ƙarar sun haɗa da na Jihohin Bauchi, Adamawa, Bayelsa, Enugu, Osun, Filato da Zamfara.

Gwamnonin suna neman Kotun da ta soke dakatarwar da aka yi wa zaɓaɓɓun mutanen inda suka kafa hujja da sakin layi na 1(2) da na 5(2) da kuma na 305 waɗanda ke kore wa shugaban ƙasa ikon dakatar da gwmna ko mataimakinsa da al’umma ne suka zaɓe su.

Haka kuma suna neman Kotun da ta ayyana hukuncin a matsayin haramtacce kuma abinda aka yi ba bisa doka ba.

Bugu da ƙari, sun ƙalubalanci ɗora Ibas a matsayin jagoran, wanda suka ce Shugaban bai da ikon yin hakan a dokance.

By Babaji