Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda a Taraba ya rasu

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

An gudanar da jana’izar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Jihar Taraba, Abdullahi Usman, wanda ya rasu a safiyar Lahadi a gidansa da ke Jalingo, babban birnin jihar. Usman Abdullahi, wanda ya shafe shekaru da dama yana aiki a matsayin kakakin rundunar, yayi fama da rashin lafiya kafin rasuwarsa.

Gambo Kwache, wanda yake riƙon muƙamin kakakin rundunar yayin da Usman ke jinya, ya tabbatar da rasuwar a ranar Lahadi. Ya bayyana cewa marigayin ya daɗe yana fama da rashin lafiya kafin ya koma ga Mahaliccinsa.

Marigayi Usman Abdullahi an riga an yi masa sallah tare da binne shi bisa tanadin addinin Musulunci. Mutuwar tasa ta girgiza abokan aiki da iyalai, yayin da jama’a ke ta’aziyyar rashin wanda aka san shi da jajircewa a aikin hulɗa da jama’a.

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Taraba ta nuna alhininta bisa wannan rashi, inda ta bayyana cewa za ta ci gaba da tuna gudummawar da marigayin ya bayar wajen inganta harkar sadarwa tsakanin rundunar da al’umma.

By ukarofi