
Daga BELLO A. BABAJI
Kimanin fursunoni 12 ne suka tsere a yayin fasa wani sashe na kurkuku a Jihar Kogi, a safiyar ranar Litinin.
Kwamishinan Labarai na jihar, Kingsley Fanwo ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyana wa al’umma cewa gwamnati da hukumomin tsaro suna iya kokarinsu wajen kauce wa faruwar irin haka a nan gaba.
Ya ce, har jami’an tsaro sun kamo ɗaya daga cikin waɗanda suka tseren.
Ya kuma ce, za a yi bincike mai zurfi don gano musabbabin faruwar al’amarin da kuma kamo sauran fursunonin.
Kwamishinan ya ƙara da cewa, Gwamna Usman Ododo na jihar ya umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da irin haka bai sake faruwa ba.
Bugu da ƙari, ya yi kira ga al’umma da su ruwaito dukkan wanda suke zargi da ya shiga cikin su, sannan za a hukunta su wanda aka kama da ba su mafaka.
Haka kuma ya nemi da su kwantar da hankula a cigaba da gudanar da harkokinsu cikin lumana yayin da hukumomi suke bincike.
