Majalisar Dattawa ba ta samu biyu bisa uku ba kafin amince wa dokar ta-ɓaci a Ribas, inji Tambuwal

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya yi ikirarin cewa Majalisar Dattawa ba ta samu mafi rinjayen adadin sanatocin da ake buƙata a dokance ba kafin ta amince ta tabbatar da dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya sanya a Jihar Ribas.

Rahotonni sun bayyana yadda Shugaba Tinubu ya sanya dokar tare da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar, mataimakiyarsa da kuma ƴan majalisar dokoki na tsawon watanni shida, sannan ya ɗora Ibok-Ete Ibas a matsayin wanda zai jagoranci harkokin shugabanci, ranar Talata.

A ranar Alhamis ne majalisar ta shirya zaman tattauna batun hukuncin dokar da shugaban ƙasar ya sanya wa jihar, inda suka amince da ita bayan zaɓen baka da suka gudanar a tsakanin su.

Lamarin da ya haifar da cecekuce acikin al’ummar ƙasa game halascin yin hakan a dokance.

A lokacin da ya ke magana da manema labarai a Abuja, Tambuwal, wanda tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ne, ya ce an yi hukuncin ne ba tare da kiyaye abinda doka ta shar’anta na samun kaso biyu bisa uku na ƴan majalisar ba kafin aka amince.

Ya bada misali da sakin layi na 305 na dokar ƙasa, wanda ya ce ya bayyana komai a sauƙaƙe game da matsalar, wadda aka gaza cike ƙa’idodinta kafin a tabbatar da ita.

Ya kuma ce ba a samu adadin sanatocin da ya kamata a ce sun yi hukunci akan batun ba a ranar da aka yi zaman, ya na mai cewa lallai ba su kai biyu bisa uku da dokar ta amince da shi ba.

By Babaji