INEC ta karɓi ƙorafin neman yi wa Sanata Natasha kiranye

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Zaɓe, INEC, ta karɓi takardar ƙorafi da ke neman yin kiranye ga Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a matsayin sanata a Nijeriya.

Sakatariyar hukumar, Rose Oriaran Anthony ce ta karɓi takardar a Abuja, wadda wasu ƴan mazaɓar Kogi ta Tsakiya masu katin zaɓe suka kai ofishin hukumar.

Takardar ƙorafin na neman a yi wa sanatar, wadda aka dakatar kiranye daga Majalisar Dokoki.

Shugabar tawagar, Charity Ijoshe Omole, wadda ta miƙa takardar, ta ce sun dawo daga rakiyar Natasha, saboda ayyukanta na rashin biyayya, waɗanda suka sanya aka dakatar da ita.

Ta ce, acikin masu katin zaɓe guda 488,000 daga mazaɓar, sama da 250,000 sun sanya hannu kan kiranyen sanatar.

Ta kuma ce, hakan ya zama wajibi domin abubuwan da sanatar ta ke yi cin mutunci ne a gare su da ma Jihar Kogi baki ɗaya.

By Babaji