
Daga BELLO A. BABAJI
An sake kama wasu mutane biyar daga cikin 12 da suka tsere daga gidan yarin Koton Ƙarfe dake Jihar Kogi.
Kakakin Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali (NCoS), DCC Umar Abubakar ya bayyana hakan a wata takarda yayin tabbatar da tsarewar fursunonin, lamarin da ya faru a safiyar ranar Litinin, 24 ga watan Maris, 2025.
Ya ce, wasu daga cikin fursunonin ne suka buɗe wasu kwaɗi na ɗaya daga cikin ƙofofin gidan yarin, wanda hakan ya yi sanadin ficewar mutane 12.
Tuni jami’an hukumar da haɗin gwiwar wasu hukumomi suka ɗauki matakan gaggawa, wanda hakan ya sa aka sake kamo wasu daga cikin su, ya na mai cewa suna cigaba da ƙoƙarin kamo sauran fursunonin.
Ya kuma ce, Kwantirola Janar na riƙon ƙwarya na hukumar ya umarci a gudanar da bincike game da musabbabin faruwar al’amarin.
Haka kuma, an inganta tsaro a gidajen yarin dake sassa daban-daban na ƙasar domin kauce wa faruwar irin haka a nan gaba.
Kazalika, NCoS ta yi kira ga al’umma da su kwantar da hankula tare da ruwaito duk wani bayani da zai taimaka masu wajen kama sauran waɗanda suka tseren.
