Haɗin Kai tsakanin gwamnati da ‘yan jarida ne zai kawo cigaba a Jihar Kano – Aminu Bala

Spread the love

A Jihar Kano, ‘yan jarida da gidajen yaɗa labarai suna da damar bayyana ra’ayoyinsu bisa ƙa’idoji da dokokin aikin jarida. Sai dai, gayyatar da ‘yan sanda suka yi wa wasu ‘yan jarida biyu na Kano Times ta haifar da cece-kuce a shafukan sada zumunta da dama.

A gaskiya, ba a kama su ba, sai dai an nemi su bayyana domin yin bayani kan labarin da suka wallafa a jaridar Kano Times, wanda ke da alaƙa da kwamishinan watsa labarai da harkokin cikin gida na Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya da wasu batutuwa.

Wasu daga cikin masu fashin baƙi sun yi nuni da cewa wannan gayyata ba ta dace ba, yayin da Amnesty International ta yi suka kan lamarin ba tare da cikakken bincike ba.

Wannan ya haifar da tambayoyi kan ingancin rahoton da ƙungiyar ta fitar.

Gwamnatin Kano dai tana mutunta ‘yancin ‘yan jarida kuma ta fahimci muhimmancin rawar da suke takawa wajen inganta dimokuraɗiyya da ci gaban al’umma.

Kwamishina Waiya, wanda aka san shi da jajircewarsa a fannin kare hakkin ɗan Adam da aikin jarida, ya jaddada cewa gwamnati na neman zaman lafiya da haɗin kai, ba rikici ba.

A ƙarshe, yana da matuƙar muhimmanci a guji yaɗa labarai marasa tushe da yanke hukunci ba tare da cikakken bincike ba. Haɗin kai tsakanin gwamnati da ‘yan jarida shine hanya mafi dacewa don ci gaban Kano da kare haƙƙin kowa.

By ukarofi