Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Janar manajan hukumar tsara biranen Karu wato Greater Karu Development Control Agency da a ka fi sani da (GKADCA) ta gwamnatin Jihar Nasarawa Esv. Yakubu Auta Haruna ya shawarci masu harkokin manyan gine-gine a yankin gabashin jihar su riƙa yin amfani da damar ayyukan hukumar a yayin da suke gudanar da ayyukan nasu.
Janar manajan hukumar yayi kiran ne kai tsaye wa masu harkar a lokacin da yake tattauna da wakilin mu a ofishin sa dake hukumar a garin Mararaba ta ƙaramar hukumar Karu a jihar.
Esv. Yakubu Auta Haruna yace akwai buƙatar kyakkyawar haɗin kai da hukumar don tabbatar da tsarin gine-gine nagari mai inganci da zai rage asara ko ganganci.
Ya bayyana cewa aikin hukumar a fannin tsara da kuma kula da manyan ayyukan bunƙasa yana da matukar mahimmanci musamman idan a kayi la’akari da kusantar yankin ga birnin tarayya Abuja.
Janar manajan hukumar ta tsara birane Esv. Yakubu Auya Haruna ya kuma bayyana cewa hukumar ta GKADCA a yanzu haka tana kulawa ne da ƙananan hukumomin jihar guda biyar da suka haɗa da Karu, kanta da Keffi da Kokona da Nasarawa da kuma Toto.
Ya jaddada mahimmancin aiwatar da manyan ayyukan cigaba cikin tsari inda ya gargaɗi al’umma baki ɗaya su guje wa fara aikin gine-ginen ba tare da sun samo izini daga hukumar ba.
Janar manajan har ila yau ya kuma bayyana wasu daga cikin dimbin nasarori da hukumar ta cimma ƙarƙashin jagorancin sa cikin kimanin watanni huɗu kacal da yayi a kujerar cewa sun haɗa da inganta da tsaftace muhalli da ofishoshin hukumar don bai wa ma’aikatan hukumar damar gudanar da ayukan su yadda yakamata a kuma cikin tsafta inda ya ƙara da cewa kafin zuwan sa ofishoshin sun kasance cikin yanayi na Allah-wadai da hakan yayi ta shafan ayyukan ma’aikatan da sauran su.
Haka kuma a fannin aiki tuƙuru da zuwa aiki cikin lokaci Esv. Yakubu Auta Haruna ya bayyana cewa sakamakon zaman faɗakarwa da yake yi akai-akai da ma’aikatan hukumar kowa cikin su yana ƙara himma da ƙwazon aiki saɓanin yadda lamarin yake a da.
Daga ƙarshe Esv. Yakubu Auta Haruna ya kuma sanar cewa a yanzu ƙalubalen da hukumar wadda mallakar gwamnatin jihar ce ke fuskanta shine na rashin ababen hawa da suke buƙata a yayin da suke gudanar da ayukan su ta sintirin duba ayukan da sauran su duk da cewar inji shi gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule yana da sanin matsalar kuma tuni ya ɗau matakan magance su.
