An ga jinjirin watan Shawwal a Saudiyya a ranar Asabar, 29 ga Maris, wanda ke nuna cewa yau Asabar zai kasance ranar ƙarshe na watan Ramadan, kuma gobe Lahadi, 30 ga Maris, zai zama ranar farko ta Shawwal.
Kotun ƙoli ta Saudiyya ta buƙaci ɗaukacin Musulmi a faɗin ƙasar da su dubi jinjirin watan Shawwal 1446AH a yammacin ranar Asabar, kamar yadda Kamfanin dillancin labaran Saudiyya (SPA) ya rawaito.
A duk da cewa ranar Eid tana iya bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa dangane da ganin wata, ana sa ran Nijeriya ma za ta yi bikin Sallah a ranar Lahadi, 30 ga Maris, 2025.
