
Daga BELLO A. BABAJI
An samu kafuwar wata jam’iyya a Nijeriya mai suna TNN, wato ‘Team New Nigeria’, wadda a yanzu haka an mata rajista, inda har ta fitar da bajinta, kirarinta da kuma takenta a yayin da ta ke ƙoƙarin shiga sahun sauran jam’iyyu a ƙasar.
Jami’yyar, wadda ke da burin haɗe kan ƙasa da sake gina ta, ta ce za ta ƙaddamar da dokokinta da manufofinta a watan Afrilu, 2025 a wani ɗakin taro a Abuja, inda za a yi mata gabatarwa ta musamman.
Kakakin TNN, Dakta Mohammed Adah Shuaibu a wata takarda, ya ce kwamitocin Zartarwa da na Amintattu ne suka amince da ‘TNN’ a matsayin sunan, yayin da taken shi ne ‘Greater Nigeria’ sai kuma kirarinta, ‘Unite and Rebuild the Nation’.
Don haka ya ce sun fara sabuwar tafiyar, wadda ta ƙunshi samar da sabuwar ƙasa da al’umma ke fatan a cimma.
A nasa jawabin, Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Modibbo Yakubu Farakwai, ya ce jam’iyyar ta cika duk wasu ƙa’idodi da sharuɗa da Hukumar Zaɓe, INEC ta tanada wajen tabbatar da ita a matsayin halastacciyar jami’yya.
Ya kuma ce, sun shirya kwamitoci da suka haɗa da na shari’a, kiyaye dokoki, gudanar da siyasa, isar da saƙo da karɓa, wayar da kai, kuɗi, yaɗa labarai, tsare-tsare, tarurruka da na zama mamba, ya na mai cewa sun tanadi ƙwararru da za su tafiyar da ayyukan kwamitocin cikin inganci.
