Na fusata da Putin akan Ukraine – Trump

Spread the love

Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna rashin jin daɗinsa da shugaban Rasha ɓladimir Putin kan kalaman baya-bayan nan game da shugabancin Ukraine.

Trump da yake magana da shugabar NBC, Kristen Welker, ya ce “ya yi matuƙar fusata” game da Putin da ya yi tambaya kan matsayin shugaban Ukraine ɓolodymyr Zelensky a matsayin jagora.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da NBC, Trump ya yi gargaɗin cewa, idan Rasha ta gaza cimma yarjejeniyar dakatar da yaƙin da ake yi a Ukraine kuma aka same ta da alhakin tsawaita rikicin, to zai sanya haraji na biyu kan dukkan man da Rasha ke fitarwa.

“Idan ni da Rasha ba za mu iya cimma matsaya ba don kawo ƙarshen zubar da jini a Ukraine, kuma na tabbatar da Rasha tana da laifi, zan sanya haraji kan duk wani mai da ke fitowa daga Rasha,” inji Trump.

Kalaman nasa sun yi nuni da samun sauyi mai ma’ana yayin da gwamnatinsa ke ci gaba da ƙoƙarin tattaunawa kan yarjejeniyar zaman lafiya, ko da yake ba a samu nasara ba. Kwanan nan Putin ya yi watsi da shawarar haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Ukraine na tsagaita buɗe wuta na kwanaki 30 tare da ba da shawarar a cire Zelensky daga muƙaminsa a matsayin wani ɓangare na duk wani kudiri.

Tun bayan komawar Trump kan karagar mulki, dangantakar da ke tsakanin Washington da Moscow, da kuma barazanar da Trump ya yi na dakatar da goyon bayan da ake yi wa Kyiɓ, sun ƙara ƙarfafa wa Rasha gwiwa a fagen daga. Jami’an Ukraine sun zargi Rasha da tsawaita tattaunawa ba tare da wata manufa ta gaskiya ta dakatar da yaƙin da take yi na soji ba.

Sabbin hare-haren da aka kai a birnin Kharkiɓ da ke kan iyaka da arewa maso gabashin ƙasar, ya kaɗa da kai hare-hare guda shida cikin dare, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka, da suka haɗa da jami’an soji da suka jikkata, da kuma fararen hula aƙalla biyu. Bugu da ƙari, sojojin na Rasha sun kwace wani kauye mai nisan kilomita bakwai kacal daga tsakiyar Dnipropetroɓsk yankin na Ukraine.

Putin wanda ya shafe shekaru 25 yana mulkin Rasha yana ci gaba da ƙalubalantar sahihancin Zelensky, saboda cikar wa’adinsa na farko na shekaru biyar a watan Mayun 2024. A ƙarƙashin dokokin Ukraine, ba za a iya gudanar da zaɓe a lokacin yaƙi ba, kuma shugabannin ‘yan adawa sun amince cewa ya kamata a gudanar da zaɓe ne kawai bayan kawo ƙarshen rikicin.

Har ila yau alaƙa ta yi tsami tsakanin Trump da Zelensky, inda a baya ya yi masa laƙabi da “mai mulkin kama karya” da kuma yin taho-mu-gama da jama’a. Duk da haka, Zelensky ya ci gaba da jajircewa wajen neman goyon bayan ƙasa da ƙasa kan Rasha. A cikin wani jawabi na baya-bayan nan, ya buƙaci ƙawayen ƙasashen duniya da su matsa wa Putin lamba kan amincewa da tsagaita buɗe wuta.

“Tun da daɗewa, kiran da Amurka ta yi na tsagaita buɗe wuta ba tare da wani sharaɗi ba yana kan teburi ba tare da mayar da martani mai kyau daga Rasha ba,” inji Zelensky, yayin da yake yaba wa da ƙasashen da suka kara takunkumi kan Kremlin.

Tun farko dai Moscow da Kyiɓ sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a tekun Black Sea bayan tattaunawa da jami’an Amurka, amma Rasha ta dage cewa dole ne a ɗage takunkumin kafin duk wata yarjejeniya ta fara aiki.

Da yake bayyana barazanar harajin nasa, Trump ya bayyana cewa ƙasashen da ke sayen mai na Rasha za su fuskanci takunkumi wajen yin kasuwanci da Amurka.

“Idan ka sayi mai daga Rasha, ba za ka yi kasuwanci a Amurka ba, za a sanya harajin kashi 25 cikin 100 a kan dukkan mai, kuma akwai yiwuwa ya ƙaru zuwa kashi 50,” inji shi.

Lamarin dai na ci gaba da taɓarɓarewa, yayin da ƙoƙarin diflomasiyya ke ci gaba da samun tazgaro, ba tare da an kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a Ukraine ba.

By ukarofi