Kisan Edo: Ina jin ihun ‘yan uwana lokacin da wuta ke cin su – Shehu

Spread the love

Wani matashi daga Kano, Abubakar Shehu, ya bayyana yadda ya tsira daga harin da aka kai wa wasu mafarauta da ya ke cikinta, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar abokansa 16. Shehu ya ce sun kasance a bayan wata babbar mota yayin da wasu ‘yan banga suka tare su. “Sun umarce mu da mu sauka daga motar, sannan ba tare da wata magana mai yawa ba, ɗaya daga cikinsu ya bugi shugaban mu da gatari,” in ji Shehu, mai shekaru 20.

Bayan haka, sun fara dukan su, amma Shehu ya ce ya samu damar kauce wa wasu bugun sannan ya gudu da iya ƙarfinsa. “Na faɗa cikin wata rami, daga nan na tashi na fake a wani gini da ba a amfani da shi na tsawon sa’o’i kafin na fito da misalin ƙarfe goma na dare,” in ji shi. Duk da haka, yana jin ihun abokansa yayin da ake dukan su sannan daga bisani aka cinna musu wuta. Daga bisani, ya samu damar tsaida wata babbar mota, wacce ta dauke shi zuwa garin su lafiya.

Bayan wannan mummunan hari, rikici ya ƙara ƙamari a ƙasar, inda ake ci gaba da kiran hukuma da ta tabbatar da adalci. Gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun buƙaci a hukunta waɗanda suka aikata wannan ta’asa. Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai cewa kowane ɗan Najeriya na da ‘yancin yin tafiya cikin ‘yanci a duk faɗin ƙasar. A halin yanzu, ‘yan sanda sun kama mutane 14 da ake zargi da hannu a wannan aika-aika, yayin da iyalan mamatan ke ci gaba da jimamin rashin masoyan su.

By ukarofi