Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Shugaban Jami’ar Sufuri ta Tarayya da ke Daura Farfesa Umar Adam Katsayal, ya ce jami’ar da ke ƙarƙashin sa ta fara ƙoƙarin ganin ta ƙara fitowa fili a tsakanin ƙasashen Afirka ta hanyar samar da damammaki daidai wa daida ga kowa da kowa don daukar Dalibai a jami’ar a kowace Ƙasa a faɗin Afirka.
Farfesa Katsayal ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da wata ƙasida a yau, Asabar mai taken “ILIMI MAI ƊOREWA: Don bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen Afirka. a taron ƙoli na ilimi na Afirka karo na uku da ke gudana a Zimbabwe wanda yake gudana a Elephant Hills Hotel, Victoria Falls, Zimbabwe.
Jawabin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun babban jami’in yaɗa labarai da sadarwa na jami’ar Umar Usman kuma aka rabawa manema labarai a Gusau.
Shahararren wuri na Victoria Falls wuri ne na tarihi na UNESCO wanda shine mafi girma a duniya kuma ya ƙunshi cibiyar ayyukan buɗe ido da kallon namun daji, wanda masu shirya taron suka ɗauka cewa ya dace da ɗaukar nauyin taron na bana.
Taken taron shine “Fassara ci gaban Iliminmu zuwa ci gaban Nahiyar Afirka: Hanyar Dabaru.”
Sanarwar ta yi nuni da cewa, taron da ake gudanarwa a halin yanzu, wani shiri ne na haɗin gwiwa, da nufin wadata nahiyar Afirka da shugabannin da suke so a nan gaba.
“A ƙarshen taron kuma ana sa ran zai zama wani dandali na bunƙasar ilimi, da haɗa kai da juna, da haɗa kai don inganta ilimi a nahiyar Afirka”. Sanarwar ta karanta a wani ɓangare.
Farfesa Kachayal ya baje koli na musamman na harkar sufurin jami’ar a Daura dake Jihar Katsina da kuma kwasa-kwasan da jami’ar ke bayarwa kasancewar ita ce irinta ta farko a nahiyar Afirka ta yadda ƙasashen Afirka za su fahimci irin damammakin da jami’ar ke bayarwa don amfanin kansu.
Shugaban ƙasar Zimbabwe Dr. Emmerson Dambudzo Mnangagwa a cikin wani muhimmin jawabi ya yi kira ga wakilai da su gabatar da tattaunawa kan ƙirƙire-ƙirƙire tare da inganta ra’ayoyin da za su ciyar da Afirka a gaba.
“Dole ne taron ya samar da ingantattun hanyoyin warware matsalolin da za su ba da damar ci gaba a nahiyar Afirka da kuma sake fasalin tsarin iliminmu don amfanin matasanmu don ci gaban Afirka,” in ji shi.
Shugaban ya ci gaba da yin kira ga mahalarta taron da su yi aiki tare domin mayar da makarantunmu masu ƙirƙire-ƙirƙire don samar da ayyukan yi ba kawai harshen turanci ba, harshen da kakanninsu ba suyi amfani da shi ba a baya.
Ya tabbatar da cewa shugabannin Afirka na yanzu a shirye suke su ba da dukkan goyon bayan daya dace don haɗa kan yaran Afirka don samun damar samun ilimi da rayuwa mai kyau.
Cibiyar Global Skills Hub, Birtaniya da masu ruwa da tsaki a harkokin ilimi na Afirka ne suka shirya miƙa taron tare da haɗin gwiwar gwamnatin Zimbabwe da kuma tallafin kungiyar Lion Outreach International.
