Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban ƙungiyar haɗin kan Funtua kwamred Mannir Suleiman yayi kira ga yan kwangilar da ke aikin hanyoyin cikin garin Funtua da su yi aiki mai inganci.
Kwamred Mannir yayi wannan magana ne a lokacin da yakai ziyarar duba yadda aikin titunan ke gudana.
Ya shawarci ‘yan kwangilar da dubi ƙa’idojin da a kai yarjejeniya a tsakanin kamfanin da gwamnatin Jihar Katsina domin kammala aikin hanyoyin akan lokaci.
Shugaban ƙungiyar ya kuma yi kira ga ‘yan kwangilar da su rinƙa zuba ruwa a inda suka ɓanbare tsohon kwaltan domin kauce wa cututtuka irin su cutar Asma da mazauna wuraren da ake ayyukan ka shafa.
Ya kuma yaba da yadda aikin ke gudana da yayi imanin cewa da zarar an kammala, harkokin kasuwanci da zumunci za su inganta.
Kwamred Suleiman ya jinjina wa Gwamna Dikko Raɗɗa bisa ƙoƙarin sa na mai da garin Funtua ya zama babban birni da zai yi gogaiya da sauran birane a ƙasar.
“Babu shakka wannan hanyoyin da gwamnatin Dikko Raɗɗa ke ganawa a garin Funtua zai kawo bunƙasa na tattalin arzikin yankin da jiha baki ɗaya, tare da magance matsalolin tsaro da ya shafi yankin”kwamred Mannir ya ce
