
Daga BELLO A. BABAJI
Jami’an rundunar ƴan sanda a Abuja, sun yi nasarar kama Rabi’u Jibril da Ibrahim Isa, waɗanda sanannun ƴan fashi ne da kuma ƙwato motoci da wasu ababe.
Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, ta ce a ranar 27 ga watan Maris ne jami’ansu da ke aiki a rukunin Mabushi suka kai ɗauki a rukunin gidaje na Royal Court Estate dake Jahi na II.
Lamarin ya biyo bayan kiran gaggawa ne da suka samu da misalin ƙarfe 3:20 na asuba, inda da isar su ne aka samu ba-takashi tsakanin su da ɓarayin.
A sakamakon haka ne ƴan sandan suka raunata wasu daga cikin ƴan fashin da suka yi yunƙurin tserewa da kuma kama biyun, waɗanda mazauna Tiper Garage ne a Jahi.
Ga wasu daga cikin ababen da ƴan sandan suka ƙwato kamar yadda Blueprint ta ruwaito: “Two locally made firearms; Three suspected stolen vehicles: Black Toyota Matrix (Reg. No. NBS 348 CP), Black Toyota Venza (Reg. No. ABJ 105 AV), and Grey Lexus IS350 (Reg. No. RSH 295 CB); Electronic devices including:Two MacBook Pro laptops, One Lenovo laptop, One iPad, One PS4 gaming console, One Canon IP1224 camera, and One drone camera.”
Ta kuma ce, a yanzu ɓarayin suna hannun ƴan sanda, inda bayan kammala bincike akan su ne za a maka su a kotu domin su fuskanci hukuncin doka.
Ta ƙara da cewa Kwamishinan ƴan sandan birnin, CP Ajao Adewale, ya yi kira ga mazauna birnin da su riƙa sanya na’urorin bin diddigi a ababen hawansu, don gano su a yayin da aka sace cikin lokaci.
Bugu da ƙari, ta bada lambobi kamar haka, domin ruwaito duk wani abin zargi da suka gani a tare da su: 08032003913, 08033111911, 07057321547.
