An rufe Hedikwatar APC ta Ƙasa bayan kashe daraktanta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jami’yyar APC ta rufe Hedikwatarta dake Abuja da ake kira da ‘Buhari House’, biyo bayan kashe daraktan gudanarwarta, AbdulRauf Adeniji.

A ranar Alhamis ne jam’iyyar ta sanar da rufe ofishin a wata takarda, sakamakon jimami na rashin daraktan.

Rahotonni sun bayyana cewa, an kashe Adeniji ne a watan da ya gabata, makonni da dama da garkuwa da shi.

Ta ce, ofishin zai cigaba da zama a rufe har zuwa ranar Litinin, 14 ga watan Afrilu.

Ta kuma yi kira ga jami’anta da su yi amfani da damar hakan wajen yi wa mamacin addu’a gami da jajenta wa iyalai da abokan arziƙinsa.

Haka kuma za a karɓi gaisuwar ta’aziyya a ofishin bayan dawowarsa aiki.

By Babaji