
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Kwamitin da Gwamnan Jihar Kano ta kafa ƙarƙashin Gwmna Abba Kabir Yusuf ya kafa don bibiyar batun kisan gillar da ya faru garin Uromi na Jihar Edo, ya bar Kano domin binciko ainihin abinda ya faru tare da tabbatar da ɗorewar zaman lafiya.
Kwamitin ya samu jagorancin ne na mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo
A saƙon da ya aika wa manema labarai mai nagana da yawun mataimakin gwamnan na Kano, Ibrahim Garba Shu’aibu, ya ce kwamitin ya ƙunshi muhimman mutane da suka hadar da Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isah Umaru da Kwamishinan Addini da na Ƙananan hukumomi da Al’amuran Masarautu da na Ayyuka na Musamman da ta Harkokin Mata da kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Bunkure da sauran manyan jami’ai.
Kafa Kwamitin ya biyo bayan fushin da al’ummar ƙasar nan suka nuna bayan mummunan harin da aka kai wa wasu matafiya a garin na Uromi wanda hakan ya yi sanadiyyar kashe mutane da dama tare da jawo wasu tserewa daga inda suke daga cikin ‘yan asalin jihar Kano dake rayuwa a yankin.
Da ya ke jawabi kafin tashi daga Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano, Mataimakin Gwamnan ya jaddada ƙudirin kwamitin na tabbatar da adalci da dorewar zaman lafiya da kuma sasanta juna.
“Aikinmu a fayyace yake – bincike, tuntuɓa da kuma bayar da shawarwari masu warkarwa. Wannan ba wai batun gano gaskiya ba ne kaɗai, amma har da gina zaman lafiya da nufin dawo da ƙarfin gwiwa da kuma kare faruwar wani tashin hankali a gaba.”
Lamarin mai tayar da hankali da ya faru a watan da ya gabata, ya haddasa zaman ɗar-ɗar a garin.
Daga cikin ayyukan da aka ɗora wa kwamitin akwai tattaunawa da Gwamnan Edo da shugabannin hukumomin tsaro da sarakuna da kuma ƙungiyoyin ci-gaban al’umma a yayin aiki na mako guda da kwamitin zai gudanar.
