Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Fadar Shugaban ƙasar Nijeriya ta nemi afuwa kan kura-kuren da aka samu a jerin sunayen naɗe-naɗe da ta fitar, wanda Shugaba Bola Tinubu ya yi tun ranar 29 ga Mayu, 2023.
An ruwaito cewa, an jera sunayen ne domin murƙushe labarin naɗe-naɗen muƙamai da Tinubu ya yi, wanda Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume ya kawo wa jama’a.
A wata hira da ya yi da Arise Television a kwanakin baya, Ndume, ɗan majalisar dokoki na jam’iyyar APC, ya zargi shugaban ƙasar da saɓa ƙa’idar tarayya wajen naɗin nasa, wanda fadar shugaban kasar ta musanta.
Don magance wannan zargi, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare, a ranar Laraba ya fitar da jerin sunayen waɗanda Tinubu ya naɗa da kuma yankunansu.
Jerin sunayen ya nuna cewa shugaban ya naɗa mutane 29 daga Kudu maso Yamma, yankin sa, 35 daga Arewa maso Yamma, 22 daga Kudu maso Kudu, 16 daga Kudu maso Gabas, 25 daga Arewa ta Tsakiya da 24 daga Arewa maso Gabas.
Sai dai masu sukar shugaban ƙasar sun nuna cewa jerin sunayen ba su cika ba, saboda sunan wani babban muƙami daga yankin shugaban ƙasar ya ɓata.
Ficewar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, da Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa, Kemi Nandap, da dai sauransu, daga cikin jerin sunayen ya ƙara ƙarfafa ra’ayin rashin daidaiton yankin a kan gwamnatin Tinubu, domin jerin sun nuna ƙarara cewa Kudu maso Gabas ba su da wakilci a gwamnatinsa.
Kamar yadda takardar ta haifar da mahawara a shafukan sada zumunta, Dare ya wallafa saƙo a shifin ɗ a ranar Alhamis don neman afuwar kura-kuran da ke cikin jerin kuma ya yi alƙawarin samar da sabbin jerin sunayen daga baya.
Sai dai kakakin shugaban ƙasar bai bayyana dalilin da ya sa aka cire sunan Gbajabiamila daga cikin jerin sunayen ba.
“Mun lura da kura-kurai da dama a cikin jerin. Muna neman afuwa. Za mu samar da sabon jerin sunayen daga baya. Na gode,” ya rubuta.
