Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Jinin al’ada, duk da kasancewarsa ɗabi’ar halitta ta rayuwa, yana ci gaba da zama babbar matsala ga karatun ‘ya’ya mata a makarantun sakandare a faɗin Jihar Yobe.
Rashin samun kayan tsaftar jinin al’ada na tilasta wa wasu ‘yan mata zaman gida a lokacin jinin su, lamarin da ke haifar da rashin halartar darussa, faduwar darajoji, da kuma rage musu ƙwarin gwiwa.
Domin shawo kan wannan matsala, Jakadiya Fatima Mohd Paga, wakiliyar UN Women ga gwamnan Jihar Yobe, ta yi kira da a kafa matattarar samar da audugar tsafta a makarantun sakandare a faɗin jihar.
A cewar Fatima Paga, samar da waɗannan matattara zai bai wa ‘yan mata damar samun kayan tsafta kyauta ko kuma a farashi mai sauƙi. Wannan tsari zai tabbatar da cewa babu wata yarinya da za ta rasa karatu saboda rashin kayan tsafta a lokacin jinin al’ada.
“Ta hanyar samar da kayan tsafta, za mu taimaka wa ‘yan mata su maida hankali kan karatu maimakon damuwa da batutuwan tsafta na yau da kullum. Wannan tallafi yana ƙara musu ƙwarin gwiwa da kuma tabbatar da daidaito wajen cimma nasara,” in ji ta.
Jakadiya Fatima ta bayyana haɗarin da ke tattare da amfani da kaya marasa tsafta kamar yadi, takarda, ko jarida, wanda wasu ‘yan mata ke amfani da su saboda rashin kayan tsafta masu kyau. Waɗannan hanyoyin suna ƙara yiwuwar kamuwa da cututtuka da kuma matsalolin lafiya na dogon lokaci.
“Samar da audugar tsafta na kare lafiyar ‘yan mata, yana kuma kare musu mutunci,” ta ƙara da cewa.
Bugu da ƙari, samar da matattarar audugar Tsafta ba kawai cika wata buƙata ba ce; yana kuma taimakawa wajen kawar da tabo kan batun jinin al’ada da kuma inganta al’adun.
Fatima Paga ta bayyana cewa samar da irin waɗannan matattara na nuni da kulawa da daidaito. Ta yi kira ga masu ruwa da tsaki, gwamnati, da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su sanya tsaftar jinin al’ada a cikin manufofin ilimi.
“Tallafa wa ‘yan mata ya fara ne da tabbatar da mutuncinsu, lafiyarsu, da kuma damar da za su yi karatu cikin kwanciyar hankali ba tare da wata shinge ba,” in ji ta.
