
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Juma’a ne ƙasar Chana ta ƙara haraji ga kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka da kaso 125.
Lamarin da ya zama salo na mayar da martani ga Shugaba Donald Trump bisa hukuncinsa na ƙara haraji ga kayan Chana da kaso 145.
Hakan ya sa yaƙin kasuwanci tsakanin manyan ƙasashen duniyan biyu ya zama barazana ga rassan kasuwancin duniya.
Sannan, Chana ta yi hakan ne la’akari da takunkumim da Amurka ta sanya wa harkar tattalin arziƙinta don rage nauyin aka ɗora mata na harajin.
Sanya takunkumin kasuwanci da Amurka ta yi ya saɓa wa dokokin ƙasa-da-ƙasa da na tattali da ma lafiyayyen hankali, kamar yadda Ma’aikatar Kuɗi ta Chana ta bayyana a wata sanarwa.
