
Daga BELLO A. BABAJI
‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da wani faston cocin ɗariƙar EKWA, Samson Nda Ali, a yankin Mararraban Aboro na Ƙaramar Hukumar Sanga a Jihar Kaduna, sun sako shi.
Saidai, sun riƙe wani mai suna Yusuf Shehu Ambi, wanda shi ne wanda ya kai musu kuɗin fansar faston, inda suka nemi a ƙara masu wasu adadi na kuɗaɗe kafin su sako shi.
A ranar 8 ga watan Afrilu, 2025 ne aka yi garkuwa da Fasto Ali a gidansa, makonni biyu bayan an naɗa shi a matsayin babban jagoran wani coci a yankin.
Da fari dai waɗanda suka yi garkuwa da shi sun nemi a biya su Naira miliyan 100 ne a matsayin kuɗin fansar.
Wani shaida daga garin ya ce, wanda ya kai kuɗin, shi ne sakataren kuɗi na cocin da faston ya ke jagoranta.
