Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Haɗin gwiwa na jami’an tsaro na ‘yan sanda, sojoji, jami’an tsaron farin kaya da jami’an tsaro na al’umma CWC da yan bijilanti sun kai farmaki a wasu ƙauyuka da ‘yan bindiga suka mamaye a ƙananan hukumomin Ɗandume da Ɗanmusa a Jihar Katsina.
Wannan bayani na ƙunshe ne a wata takardar sanarwar ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labarai na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu.
Ƙauyukan sun haɗa da Dutsen Wori a ƙaramar hukumar Ɗandume inda bayan samun bayanan sirri, jami’an tsaron ƙarƙashin jagorancin DPO na Ɗandume suka afkawa yan bindigan, a nan take suka kashe ƴan bindiga biyar da gano baburan da ƴan bindigan ke amfani da su guda bakwai. Inji DSP Sadiq.
“A ƙauyukan unguwar Adam da unguwar Judo a ƙaramar hukumar Ɗanmusa bayan da hukumar tsaro na DSS suka sami bayanan sirri nan haɗin gwiwa na jami’an tsaro ƙarƙashin jagorancin DPO na Ɗanmusa suka afkuwa ƴan bindigan”DSP sadiq ya ce.
Ya ce jami’an tsaron sun sami nasarar kama mutane uku masu taimakawa yan bindigan wajen basu bayanan sirri da gano baburan biyu da keken hawa biyu na ƴan bindigan da suke amfani da su.
Jami’in yaɗa labaran ƴan sandan ya bayyana cewa jami’an tsaron na farauta sauran ƴan bindigan da suka gudu.
DSP Abubakar sadiq ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar CP Bello Shehu ya jinjina wa jami’an tsaron bisa nuna ƙwarewa da jarumta da suka nuna a yayin da suke fafatawa da yan bindigan.m
