Za a rusa gidaje 700 a aikin hanyar Legas zuwa Kalaba

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta saka wa gidaje 700 alamar rusau a babbar hanyar Legas zuea Kalaba, gabanin aikin da ake yi na gyaran hanyar.

Shugaban ayyuka na jihar Legas, Mrs Olukorede Kesha, ta bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki kan aikin babbar hanyar Legas zuwa Kalaba da ake yi.

A cewarta, adadin ya yi ƙasa sosai fiye da kiyasin farko.

“Maimakon mu ruguza gidaje kusan 1,500, mun bi hanya mafi sauƙin tattalin arziki, yanzu an bar mu da gidaje ƙasa da 700 da za a rushe,” inji ta.

Ta yaba da irin gudu-gurbi da tsare-tsare na aikin, inda ta bayyana cewa an bayar da sashe na 1 na babbar hanyar Legas zuwa Calabar mai tsawon kilomita 47 da 400 a wani lokaci da ya wuce.

Da yake magana game da daidaitawa da rusa kadarori, Kesha ya ce mutane da yawa sun koka game da daidaita tsarin, amma ba wajibi ne su bi duk wani daidaito ba.

“An kee shi lokacin da wani zai yi, amma yanzu da yake ita ce Gwamnatin Tarayya, dole ne mu duba mafi dacewa, mafi kyawun hanyar tattalin arziki,” inji ta.

Tun da farko, Ministan Ayyuka, David Umahi ya bayyana cewa babbar hanyar Legas zuwa Kalabaa ba kawai za ta kawo sauyi ga yanayin sufurin Nijeriya ba, har ma da samar da iskar carbon ta hanyar gine-gine da zanen sa.

Ya bayyana cewa, hanyar za ta sauƙaƙa cunkoson ababen hawa tare da hada ababen more rayuwa na sufuri.

“Wannan aikin zai kawar da duk wani zirga-zirgar ababen hawa daga cikin garin, kuma hakan zai zama babban abin alfahari a gare mu, ba don yau kawai muke yin gini ba, muna kuma ginawa na gobe. Kuma, ba shakka, za a yi layin dogo a tsakiya, tsakiyar tazarar mita 12 ne,” inji shi.

Ministan ya ƙara da cewa wasu yankunan kuma za su samu tashoshin jirgin kasa da kuma kayayyakin more rayuwa a nan gaba.

Da yake bayani a kan ƙalubalen da ake fuskanta a sashe na biyu na aikin, Umahi ya ce, samar da ababen more rayuwa na masana’antu na da babban ƙalubale, inda ya ce a matatar Dangote, mutum yana buƙatar izinin kusan mita 60 domin manyan motocin shiga da fita.

By ukarofi