Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A wani gagarumin mataki da ya ɗauka dangane da tashe-tashen hankulan da ke faruwa a jihar Filato, Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IGP), Dakta Kayode Adeolu Egbetokun, ya bayar da umarnin a gaggauta tura ‘yan sanda na musamman zuwa ga al’ummomin da abin ya shafa.
Wannan matakin dai na zuwa ne bayan wasu munanan hare-hare da aka kai a ƙaramar Hukumar Bokkos da kewaye, wanda aka fara tun a ranar 28 ga Maris, 2025, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da dama.
Domin jagorantar shiga tsakani, IGP ya umurci Muƙaddashin Sufeto-janar na ‘yan sanda mai kula da ayyuka, DIG Kwazhi Dali Yakubu, da ya zarce zuwa jihar Filato. DIG Kwazhi ya isa jihar ne a ranar Talata 8 ga Afrilu, 2025, inda ya kai ziyarar ban girma ga Gwamna Caleb Mutfwang.
A yayin taron, ya miƙa saƙon ta’aziyyar IGP ga iyalan waɗanda abin ya shafa da ɗaukacin al’ummar Jihar Filato, tare da jaddada aniyar rundunar ‘yan sandan Nijeriya na maido da zaman lafiya da adalci.
Tura rundunar sun haɗa da ƙarin ƙwararrun runduna, jirage marasa matuƙa don sa ido ta sama, masu ɗaukar makamai masu sulke (APCs), jirage masu saukar ungulu, rundunar ‘yan sanda na tafi da gidanka, da ƙwararrun tawaga na musamman daga Sƙuad Intervention Sƙuad (SIS). Ana sa ran waɗannan matakan za su ƙarfafa ayyukan tsaro a Bokkos da yankunan da ke makwabtaka da su inda ake ci gaba da kai hare-hare.
Hakazalika, IGP ɗin ya ba da umarnin a ɗauki matakai daban-daban domin tinkarar rikicin — ba wai kawai a daƙile tashe-tashen hankula da ake fama da su ba, har ma da hana aukuwar al’amura a nan gaba ta hanyar tattara bayanan sirri da kuma haɗa kan al’umma.
Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar, ta jaddada shirin NPF na yin aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin jihar Filato, da al’ummomin yankin, da sauran jami’an tsaro domin magance musabbabin rikicin da kuma dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.
An buƙaci mazauna yankin da su bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar samar da sahihin bayanai da za su taimaka wajen gudanar da bincike da kuma ƙoƙarin samar da zaman lafiya. Rundunar ‘yan sandan ta bai wa jama’a tabbacin cewa sun jajirce wajen kare rayuka da dukiyoyi a faɗin jihar.
