Gwamnatin Tarayya ta hana haƙar ma’adinai a Zamfara bisa cutar gubar dalma

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta umarci masu haƙar ma’adanai a jihar Zamfara ba bisa ƙa’ida ba, da su dakatar da ayyukansu kuma su fice su bar wuraren da suke haƙar ma’adanan.

Wannan na zuwa ne bayan tabbacin da aka samu na ɓarkewar cutar gubar dalma a cikin ƙaramar Hukumar mulki ta Bungudu.

Ministan tama da karafa na ƙasar Dele Alake, shi ne ya sanar da hakan to amma ya ce za a koma ci gaba da hakar ma’adinan da zarar an kammala tantance abin da ya janyo ɓarkewar cutar ta gubar dalma.

Masu haƙar ma’adinai a kasar sun ce ba su tsammaci ɗaukar matakin ba sai kawai suka ji shi kwatsam, to amma duk da haka za su bi umarnin da aka ba su domin su suna haƙar ma’adinai nai bisa ƙa’ida.

Alake ya ce, ɓarkewar lamarin wata shaida ce da ke nuna cewa cibiyoyin gargajiya da na gida sun ba wa masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida damar gudanar da ayyukansu a yankunansu ba bisa ƙa’ida ba.

A wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai Segun Tomori ya fitar, ministan ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ba ma’aikatar za ta saki wasu manyan jami’an SOP na aikin haƙar ma’adinai a Zamfara.

A wani labarin kuma, Majalisar Dokokin Jihar Oyo, a jiya, ta yi kira da a aiwatar da doka ta 001 ta hanyar da ta dace domin daƙile illolin da ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a sassan jihar.

A watan Oktoban 2023, Gwamna Seyi Makinde ya rattaba hannu kan dokar zartarwa mai lamba 1 ta shekarar 2023, da nufin kare al’ummomin da ke haƙar ma’adanai daga rashin tsaro da cin zarafi, wanda ke nuna wani muhimmin mataki na tabbatar da cewa ayyukan haƙar ma’adinai sun amfana da al’ummomin yankin da kuma gudanar da su cikin gaskiya.

ƙudurin wanda Anthony Ogunsola, mai wakiltar mazaɓar jihar Iwajowa, da Olorunpoto Cephas, na mazabar Oyo Gabas/Yamma, ya gabatar da shi, ya zo ne a zaman majalisar, wanda shugaban majalisar, Adebo Ogundoyin ya jagoranta.

‘Yan majalisar sun bayyana bukatar jihar ta sa baki domin magance matsalar rashin tsaro da ayyukan haƙar ma’adanai ke haifarwa ga al’umma musamman a shiyyar Oke-Ogun, Oyo da Ogbomosho, wadanda ba su ci gajiyar aikin hakar ma’adanai ba tsawon shekaru 30 da suka gabata.

Sun kuma nemi hanyoyin samar da kuɗaɗe don ci gaban al’umma a waɗannan yankuna.

Majalisar ta buƙaci gwamnatin jihar da ma’aikatar ma’adanai ta tarayya da su haɗa kai kan hanyoyin yaƙi da hakar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, inda ta umarci kwamitin majalisar kan daftarin ma’adinan da ya gudanar da cikakken bincike kan fannin haƙar ma’adanai a jihar domin tabbatar da aiwatar da wannan doka mai inganci.

By ukarofi