Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Muftwang ya yi tir da hare-haren da ake kai wa wasu yankuna a jiharsa, inda ya ce ‘yan bindiga sun kwace garuruwa 64.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata hira da gidan talabijin na Channels.
“Waɗannan al’ummomin da aka kai wa hari a baya-bayan nan na cikin al’ummomin da aka kai wa hari a shekarar 2023 amma sun tsira da rayukansu, suka sake gina kansu.
“Al’ummar Ruwi da aka fara kai wa hari sun yi asarar kusan mutane 17 a shekarar 2023 amma sai suka koma don nuna jajircewar mutanen,” inji gwamnan.
Sama da mutane 50 ne aka kashe a cikin mako guda a hare-haren da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai ga ƙona gidaje sama da ɗari uku a wasu ƙauyuka biyar.
Gwamnatin jihar Filato ta bakin Sakataren Gwamnatin Jihar, Samuel Jatau, ta kuma ziyarci wasu daga cikin al’ummar da abin ya shafa domin tantance irin ɓarnar da aka yi tare da bayar da tallafin kayayyakin agaji ga waɗanda abin ya shafa.
Adu ya bayyana ƙudirin Gwamnatin Tarayya na lalubo hanyoyin magance hare-hare da kashe-kashe da a ke yi.
Sai dai gwamnan ya ce hare-haren da suka addabi yankin Arewa ta Tsakiya ba sabon abu ba ne. Ya ce sama da shekaru 10 kenan jihar ke fama da irin wannan matsalar amma ba ta ɗauki hankalin al’umma ba.
“Idan an shafe kusan shekaru 10 ana kai waɗannan hare-hare, hakan yana nuna muku cewa akwai wani shiri da gangan, na kawar da jama’a.
“Kamar yadda nake magana da ku, akwai al’ummomi aƙalla 64 da ‘yan bindiga suka kwace a Filato tsakanin ƙananan hukumomin Bokkos, Barkin Ladi da Riyom.
“An karɓe su, an canja suna kuma mutane suna zaune a can cikin sauki a filayen da suka tura mutane su mamaye,” inji gwamnan.
