Sojojin ruwa sun kama lita 400,000 na ɗanyen mai da aka sace

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Sojojin Ruwan Nijeriya sun kama sama da lita 400,000 na ɗanyen mai da aka sata a cikin wata guda.

Rundunar sojin ruwan Nujeriya ta Operation Delta Sanity II ta samu gagarumar nasara a ayyukanta na yaƙi da satar mai, inda ta kwace sama da lita 400,000 na ɗanyen mai da aka sace a watan Maris ɗin shekarar 2025 kaɗai.

Sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojojin Ruwa ta Nijeriya Commodore A Adams-Aliu ya fitar ta bayyana hakan a Abuja.

A cewarsa, “Ayyukan yaƙi da satar ɗanyen mai da sojojin ruwan Nijeriya ke ci gaba da yi mai taken Operation DELTA SANITY II ya samu gagarumar nasara a cikin watan Maris 2025.”

Ya ce nasarorin da aikin ya samu sun haɗa da kwace litar ɗanyen mai 100,000 a kusa da gidan mai na Egbessan, ƙaramar hukumar Ilaje ta jihar Ondo a ranar Talata, 25 ga Maris, 2025.

“Bugu da ƙari, an gano lita 70,000 na ɗanyen mai, lita 25,000 na AGO da aka tace ba bisa ƙa’ida ba, da kuma lita 15,000 na kananzir da aka tace ba bisa ƙa’ida ba a kusa da Ndoni, Ogba, Ohaji, da Egbema West a jihar Ribas a ranar Alhamis, 27 ga Maris, 2025.

Commodore Adams-Aliu ya bayyana cewa, “Rundunar sojin ruwa ta Nijeriya za ta ci gaba da ƙarfafa ayyukanta na tallafawa harkokin tattalin arzikin Nijeriya, musamman wa’adin inganta harkar ɗanyen mai kamar yadda shugaban ƙasa kuma Babban Askarawan ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya umarta.”

Ya ƙara da cewa, babban hafsan sojin ruwa, ɓice Admiral Emmanuel Ikechukwu Ogalla, ya jaddada ƙudirin rundunar na ƙarfafa ayyukanta na tallafawa harkokin tattalin arzikin Nijeriya, musamman wajen inganta haƙo ɗanyen mai.

By ukarofi