
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar sojojin ƙasa ta naɗa Laftanal Kanal Anele Onyinyechi Appolonia a matsayin Daraktan harkokin yaɗa labarai na riƙon ƙwarya.
Ita ce mace ta farko da ta taɓa riƙe muƙamin a tarihin rundunar.
Laftanal Kanal Anele, wadda tana ɗaya daga cikin ƴan diɓa na rukunin 15 na kai-tsaye, wato ‘Direct Regular Course 15’ kuma mamba a Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Ƙasa (NIPR), ta maye gurbin Manjo-Janar Onyema Nwachukwu ne a muƙamin, wanda aka bai wa muƙami a Cibiyar Sojoji da ke kula da al’adu da manufofinsu na nan gaba.
Naɗin nata zai fara aiki ne daga ranar 22 ga watan Afrilu, 2025.
Gabannin naɗa Anele, ta yi kwas na watanni shida a Cibiyar Albarkatun Sojoji, inda daga bisa aka tura ta ɓangaren hulɗa da al’umma na rundunar.
Haka kuma ta riƙe muƙamin kakaki a ofishin Shugaban Sojojin ƙasa kafin a ba ta sabon muƙamin.
