Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa kuma ɗan takarar kujerar Shugaban ƙasa a jami’iyyar PDP a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya mayar wa gwamnonin jam’iyyar PDP martani kan ƙin amincewa da haɗaka da wata jam’iyyar siyasa.
“Haƙiƙa, jirgin haɗaka ya bar tasha kuma zai samu fasinjoji da yawa, don ɗauko ‘yan Nijeriya daga kowanne zango,” Atiku ya rubuta a shafinsa na ɗ.
Wannan tsokaci na nuni ne da cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa da jam’iyyarsa ta siyasa sun raba hanya wajen tunkarar zaɓen 2027.
Ya kuma bayar da wata alama ta yiwuwar ficewa daga jam’iyyar PDP domin ya gane yunƙurinsa na tsayawa takara.
Ya ce, “Duk abin hawar da ba zai kai mu ga shugabanci na gari a makomar ‘ya’yanmu da jikokinmu ba, to ba mota hawa ba ce”.
Mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na aasa (kudu maso kudu) Dan Orbih ya ɗora alhakin tsawaita rikicin jam’iyyar a kan sha’awar tsayawa takara a kowane zaɓen shugaban ƙasa ba tare da mutunta tanade-tanaden kundin tsarin mulkin PDP ba.
Kodayake bai bayyana cikakken ra’ayi ba, Atiku ya taɓa tsaya wa takarar Shugaban ƙasa sau biyu a PDP da kuma sau ɗaya ta hanyar amfani da rusasshiyar jam’iyyar ACN.
A cikin sanarwar da suka fitar bayan taron da suka yi a Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo, ranar Litinin, gwamnonin PDP sun ce sun yanke shawarar ƙin amincewa da hazakar, bayan tuntuɓar juna da dukkan sassan jam’iyyar PDP.
Sai dai a wata ganawa da tawagar jam’iyyar PDP daga jihar Nasarawa, Atiku ya dage cewa jirgin haɗakar ya bar tasha.
