Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sake zafafa hare-haren wuce gona da iri yayin da aka kai wa wasu ƙauyuka aƙalla uku hari a ƙaramar Hukumar Otukpo ta jihar Benuwai a ranar Laraba.
ƙauyukan da abin ya shafa a lokacin sabbin hare-haren sun haɗa da Emichi, Odudaje, da Okpamaju duk a Otukpo inda aka kashe mutane biyar a watan Fabrairu.
Al’ummomin sun fuskanci hare-hare a lokaci guda kwana guda bayan kashe mutane 11 a ƙauyen Otobi da ke ƙaramar hukumar Otukpo.
Majiyoyin cikin gida sun tabbatar da cewa mai yiwuwa an kashe mutane da dama a sabon harin.
Harin na ranar Laraba ya zo ne sa’o’i bayan Gwamna Hyacinth Alia ya tabbatar da kama wasu mutane uku da ake zargi da kai farmaki ƙauyen Otobi a daren ranar Talata.
Da aka tuntuɓi shugaban ƙaramar hukumar Otukpo, Maɗwell Ogiri, ya tabbatar da harin da aka kai wa al’umomin uku, inda ya ce maharan sun afkawa al’umomin ne a daidai lokacin da kwamishinan ‘yan sandan ke cikin fadar Ochidoma kan harin da aka kai wa Otobi a ranar da ta gabata.
Ya ƙara da cewa mutane uku ne suka samu raunuka a hare-haren da aka kai wa al’umomin uku, lamarin da ya kai mata da ƙananan yara suka bar yankunan saboda fargabar kashe su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Sewuese Anene, ya zuwa yanzu bai tabbatar da cikakken bayanin harin da aka kai wa al’umomin uku ba.
