
Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana rashin jin-daɗinsa game da sanya dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas da Shugaba Bola Tinubu ya yi.
A watan da ya gabata ne Shugaba Tinubu ya sanar da sanya dokar sakamakon rikicin siyasa da ya yi ƙamari gami da barazanar tsaro da suka haɗa da fashewar layukan mai a jihar.
Lamarin da suka sabbaba Tinubu ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa gami da baki ɗaya mambobin majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.
Daga nan ne ya naɗa VA Ibok-Ete Ibas a matsayin kantoman da zai jagoranci harkokin shugabanci a jihar har zuwa lokacin da za a warware matsalolin siyasar, lamarin da ya haifar da cecekuce acikin al’umma.
Tun lokacin da aka zaɓi Fubara a matsayin gwamnan jihar a shekarar 2023 ne aka fara samun tsama tsakanin sa da Wike na gwagwarmayar juya al’amuran siyasa da wasu tsare-tsare a jihar.
Haka kuma rikicin nasu ya shafi majalisar dokoki inda aka samu mambobi 27 sun sauya sheƙa zuwa Jami’yyar APC da kuma tsagewar majalisar zuwa gida biyu.
A yayin ganawa da manema labarai a ranar Juma’a, Wike ya bayyana cewa, ya so ne a cire Fubara daga muƙamin ba dakatar da shi ba, amma kasancewar Shugaba Tinubu ya yi hakan ne saboda maslahar al’ummar jihar, hakan ya yi daidai.
