Ƙungiyar matasa ta Arewa (AYCF) ta bayyana goyon bayanta ga Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa yadda yake jajircewa wajen ci gaban jihar ta hanyar haɗin gwiwa da bankin duniya. Shugaban ƙungiyar, Yerima Shettima, ya bayyana cewa wannan haɗin gwiwa ya haifar da ayyuka guda takwas masu muhimmanci da kuɗinsu ya kai dala miliyan 885, waɗanda za su taimaka matuƙa wajen magance matsalolin cigaba da jihar ke fuskanta.
Shettima ya tuna da yadda gwamnan ya gabatar da wata cikakkiyar manufa ta aiwatar da ayyukan yayin ziyarar da Mr. Ousmane Diagana, mataimakin shugaban bankin duniya na Yammacin da Tsakiyar Afirka, ya kai masa. Ayyukan da aka haɗa da su sun haɗa da AGILE, SURWASH, da NG-CARES, waɗanda suka shafi ilimi, lafiya, tsaftar muhalli, da kuma farfado da tattalin arziki bayan annobar COVID-19.
Shugaban na AYCF ya ce waɗannan ayyuka sun buɗe ƙofar damarmaki ga matasa da sauran al’umma, kuma ƙoƙarin gwamnan na faɗaɗa wannan haɗin gwiwa zuwa sabon shirin SPIN da RAM ya nuna irin hangen nesa da jajircewar gwamnan wajen gina tattalin arzikin da ya dace da zamani. Ya kuma buƙaci jama’a da su bada haɗin kai domin a samu nasarar wadannan ayyuka da suka ƙunshi ci gaba mai ɗorewa.
A ƙarshe, AYCF ta yabawa Mr. Diagana bisa yadda ya nuna gamsuwa da jagorancin Gwamna Uba Sani da kuma yadda aka tsara aiwatar da ayyukan vankin duniya a Kaduna. Ƙungiyar ta buƙaci dukkan jama’ar jihar su haɗa kai da gwamnati domin tabbatar da an cimma manufofin ci gaba, musamman ga talakawa da marasa galihu.
