Gwamnan Jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya bayyana cewa duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane a jihar zai fuskanci hukuncin kisa ta hanyar rataya. Ya bayyana hakan ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a zauren taro na Uromi, inda ya gana da shugabanni da mambobin al’ummar Arewa dake yankin Esan.
Gwamnan ya bayyana cewa majalisar dokokin jihar ta amince da ƙudirin dokar da ta sabunta dokar hana garkuwa da mutane ta shekarar 2013, wanda ke tanadar da hukuncin kisa ga masu aikata laifin da kuma rushe duk wani gini ko dukiya da aka yi amfani da shi wajen aikata laifin.
Okpebholo ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci rashin tsaro ba, kuma zai ɗauki matakin hukunta duk wani da ke da hannu cikin kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar. Ya ƙara da cewa za a kafa ofisoshin ‘yan sintiri a kan filayen da aka ƙwace daga hannun masu laifi, domin tabbatar da tsaro a cikin al’umma.
A nata ɓangare, al’ummar Arewa da ke jihar sun yaba wa Gwamna Okpebholo bisa matakin da ya ɗauka na tabbatar da zaman lafiya, musamman yadda ya shawo kan rikicin da ya auku a Uromi. Shugaban kasuwar shanu ta Uromi, Isah Muhammad, ya gode wa gwamnan bisa yadda ya rage tashin hankali a yankin, yayin da tsohon janar Cecil Esekhaigbe (rtd) ya bukaci shugabannin Arewa su tanadi bayanan sirri na mambobinsu domin kauce wa laifuka.
