Shugaban majalisar wakilai ya ƙaddamar da kwamitin mambobi 21 don sa ido kan dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar wakilai ta kafa kwamitin wucin-gadi na mutum 21 don sanya ido kan aiwatar da dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas.

Da yake ƙaddamar da kwamitin a ranar Talata, Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa wannan matakin na nuna “sadaukarwar majalisar wajen tabbatar da shugabanci na gaskiya da bin doka a ƙasarmu.”

A ranar 18 ga Maris, Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas, yana mai cewa rikicin siyasa ne ya tilasta hakan.

Har ila yau, shugaban ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara; mataimakiyarsa, Ngozi Odu; da dukan mambobin majalisar dokoki ta jihar har na tsawon watanni shida.

Shugaban ya naɗa Ibok-Ete Ibas, tsohon hafsan rundunar sojin ruwa, a matsayin shugaba na riƙon ƙwarya na jihar.

Bayan naɗinsa, Ibas ya dakatar da dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa da Fubara ya naɗa.

A yayin taron ranar Litinin, Abbas, wanda ya bayyana goyon bayansa ga dokar ta-ɓacin, ya tuna da irin wannan mataki da aka ɗauka a zamanin wasu gwamnatoci da suka gabata, musamman a lokacin mulkin Olusegun Obasanjo, inda aka dakatar da wasu gwamnoni masu ci.

By ukarofi