Yan sanda sun ceto mutane 10 daga hannun ‘yan bindiga a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina sun ceto mutane 10 da ‘yan bindiga su kai ƙokarin sacewa a babbar hanyar Faskari zuwa Gusau.

‘Yan bindigan sunyi ƙoƙarin awon gaba da motar haya ƙiran Golf ɗauke da fasinja mutum 10.

Da samun bayanan sirri game da ƴan bindigan a wannan ƙauye ƴan sandan ofishin Faskari suka kawo ɗauki tare da fatattakan ƴan bindigan.

Ƴan sandan sun sami nasarar ceto fasinjan mutane takwas da direba guda biyu na waɗannan motocin hayar guda biyu ba tare da wani ya sami rauni ba.

Kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sanda DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya faɗa a wata takardar sanarwa da ya fitar, yanzu haka ƴan sandan sun bi waɗannan yan bindiga da ƙoƙarin Kama su.

Kwamishinan yan sanda na Jihar Katsina CP Bello Shehu ya yaba wa ƴan sandan bisa ƙwarewa da ɗaukan mataki bayan samun bayanan sirri game da ƴan bindigan a wannan ƙauyen.

CP Bello Shehu ya jaddada ƙudirin rundunar ƴan sanda a jihar na kare rayuka da dukiyar al’ummar jihar.

Sai yayi kira ga al’ummar jihar da su taimakawa jami’an tsaro wajen basu bayanan sirri da zai taimaka wajen gano waɗannan ɓata gari.

By ukarofi