Yan sanda sun tarwatsa ‘yan fashi tare da kashe ɗaya daga cikinsu a Kebbi

Spread the love

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi

‘Yan sanda a ƙaramar hukumar Dandi da ke Jihar Kebbi sun sami nasarar tarwatsa wani gungun ‘yan fashi da suka addabi al’ummar Marina inda suka sami nasarar kashe mutum daya daga cikin ƴan fashin.
Kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan Jihar Kebbi SP Nafi’u Abubakar ya labartawa manema labarai, bayan da ƴan sanda daga ƙaramar hukumar Dandi suka sami labarin da misalin ƙarfe biyu na dare ranar Asabar ɗin da ta gabata ne, babban jami’in ƴan sanda da ke garin Kamba ya jagoranci ayarin ƴan sanda da ƴan sa kai suka kai samame inda suka suka sami nasarar tarwatsa gungun ƴan fashin na mutane huɗu kuma suka sami nasarar kashe mutum ɗaya tare da samun ƙaramar bindiga ƙirar (Bareta pistol) da harsashi uku.
Kwamishinan ƴan sandan Jihar Kebbi Bello M Sani ya yabawa ƴan sandan da ƴan sa kai bisa ga ƙoƙarin da suka yi na amsa kira kai tsaye ba tare da ɓata lokaci ba.
Ya yi kira ga al’umma da su rinƙa sanar da hukumomin tsaro duk wani abu da ba su yarda da shi ba, su daina ɗaukar doka a hannun su.

By ukarofi