Abin fashewa ya yi sanadin mutuwar yara biyu a Kaduna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wani ɗan shekara 13 mai suna Imam da wata Nasrin ƴar shekara 6 sun rasu a yayin da wani abin fashewa ya tarwatse a yankin Abakpa dake Jihar Kaduna.

Haka kuma wasu uku sun raunata a yayin aukuwar lamarin, ranar Talata.

Wani shaida da ya buƙaci a sakaye sunansa ya ce, ya ji ƙarar abin fashewar ne a lokacin da ya ke wanka, lamarin da ya sa ya fito a guje.

Ya ce, an yi ƙoƙarin kai Imam asibiti, saidai ya rasa ransa a gabannin haka.

Faruwar al’amarin ya jefa tsoro acikin al’ummar yankin yayin da suke zaman ɗar-ɗar.

By Babaji