
Daga BELLO A BABAJI
Wata babbar kotu a Jihar Kano ta yanke wa wani ɗan shekara 22 mai suna Sagiru Rijiyar Zaki hukuncin kisa ta hanyar rataya biyo bayan kashe kishiyar mahaifiyarsa, wato Rabiatu Sagiru sakamakon daɓa mata wuƙa da shaƙe wuyar shaƙiƙiyarsa mai suna Munawwara har lahira.
Rahotonni sun bayyana cewa, matashin ya na zama ne a ƙauyen Kutama dake Ƙaramar Hukumar Gwarzo, wanda aka tabbatar masa da aikata laifin.
A yayin hukuncin, Alƙali Amina Adamu Aliyu ta ce binciken da aka gudanar akan wanda ake zargin sun tabbatar da cewa ya aikata laifin don haka ta yanke masa hukuncin kisa.
Da farko Lauyan da ya gabatar da ƙarar, Lamiɗo Abba Soron-Ɗinki ya bayyana wa kotun cewa, matashin ya aikata laifin ne a ranar 7 ga watan Junairu, 2023 a unguwar Rijiyar-Zaki dake jihar.
Ya ce, ya ƙashe mutane biyun ne sakamakon rashin fahimta da ya shigar tsakaninsu.
Duk cewa an gabatar da shaidu biyu don su tabbatar da laifin akansa, amma matashin ya musanta aikata laifin.
