Egbetokun ya bada umarnin janye wa masu ƙumbar susa ‘yan sandan kwantar da tarzoma

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Babban Sufetan ‘yan sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin gaggawa na janye duka jami’an Police Mobile Force (PMF) daga hannun masu faɗa aji da sauran mutane masu zaman kansu a faɗin ƙasar nan. Wannan umarni ya fito ne yayin wani taro da shugabannin PMF domin sake duba dabarun yaƙi da matsalolin tsaro da ke ƙara ta’azzara a ƙasar.

Egbetokun ya jaddada cewa dukkan shugabannin rundunonin PMF za su fara aiwatar da wannan mataki ba tare da ɓata lokaci ba, yana mai cewa a hankali za a janye jami’an daga ayyukan da ba su da nasaba da tsaron ƙasa kai tsaye.

Egbetokun ya bayyana cewa an karkatar da ma’aikatan PMF daga ainihin aikinsu na yaƙi da rikice-rikice da bada tallafin gaggawa ga jihohi, zuwa yin gadin mutane masu zaman kansu. Ya ce hakan yana rage ƙarfin rundunar wajen mayar da martani a lokutan buƙata.

Ya ƙara da cewa tuni an fara sake fasalin rundunar PMF domin tabbatar da inganci da maida hankali wajen kare lafiyar al’umma da yaƙi da laifuka. Yanzu haka kowacce runduna na da umarnin zama cikin shiri da kayan aiki domin fuskantar duk wata barazana.

Bugu da ƙari, babban sufetan ya bayyana shirin kafa sabon rukuni na musamman mai suna Special Intervention Squad (SIS) wanda zai taimaka wajen tunkarar matsalolin tsaro a yankuna masu haɗari kamar Kudu maso Gabas da Arewa maso Gabas.

Egbetokun ya jaddada cewa dole jami’an PMF su koma matsayin da aka kafa su dashi — na zama rukunin yaƙi da tashin hankali mai tsari da ƙwararru. Ya kuma gargadi shugabanni da za a rika daukar su da alhakin duk wani rashin da’a daga jami’ansu, inda ya ce sabon babi ne na ladabtarwa da inganta ɗabi’a da aikin ɗan sanda.

By ukarofi