
Daga BELLO A. BABAJI
A ƙoƙarinsa na kawo ƙarshen matsalolin rashin tsaro, Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago ya sanya dokar hana fita a Minna, babban birnin jihar.
Gwamnan ya ce, daga yanzu babu zirga-zirgar ga babura da adaidaita sahu da ake aikin neman kuɗi da su da wasu daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safe.
Ya bayyana hakan ne a yayin taron masu-ruwa-da-tsak kan harkokin tsaro da wasu jagororin al’umma a Gidan Gwamnatin jihar, ranar Talata.
Saidai, an ware masu aikin gaggawa na musamman ga marasa lafiya da makamantansu.
Bago ya ƙara da cewa, lamarin tsaro a birnin da wasu sassan jihar ya yi ƙamari, inda ya umarci jagororin al’umma da su riƙa ta tantance waɗanda suka kawo masu ziyara, ya na mai cewa za a hukunta duk wanda aka samu da hannu a bai wa mai laifi mafaka.
Ya kuma ce, gwamnatinsa tana iya bakin ƙoƙarinta wajen ɗaukar matakan da suka dace a ƙoƙarinsu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma daga tashin-tashina don tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.
