Kaduna: Gwamna Uba Sani ya ƙwato filayen makarantun da gwamnatin El-Rufa’i ta sayar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

An samu fargaba a tsakanin mazauna wasu yankunan Jihar Kaduna biyo bayan umarnin Gwamna Uba Sani na karɓe gidajen wasu makarantu da filayen da aka raba a Kwalejin Alhuda-huda dake Zariya da Kwalejin Queen Amina da Kwalejin Government Commercial College, Zaria, waɗanda tsohuwar gwamnatin jihar ƙarƙarshin jagorancin Malam Nasiru El-Rufa’i ta sayar da su.

A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Sakataren Gwamnatin jihar, Dakta Abdulƙadir Mu’azu Meyere, ya ce an ƙwace gidaje da filayen ne sakamakon rashin fifita buƙatun al’umma da kuma duba maslaharsu.

Ya kuma ce, tuni gwamnatin ta fara shirye-shiryen mayar wa mutanen da hakan ya shafa kuɗaɗensu na gidajen da suka saya.

Sakataren ya ƙara da cewa, hakan zai taimaka wajen samar da yanayin karatu mai kyau ga ɗalibai a jihar a ƙoƙarin gwamnan na inganta rayuka da harkokin jama’a.

A bisa yunƙurin ne Gwamnan, a shekarar 2023 ya rage kuɗaɗen ɗaukar karatu ga ɗaliban manyan makarantu gami da gina ajijuwa da dama da gyara wasu da dai sauransu don ganin ya bunƙasa harkokin ilimi a jihar.

By Babaji