
Daga BELLO A. BABAJI
Wani ɗan ta’adda ya harbe makiyayi mai suna Hamza Sulaiman har lahira a yayin da ya ke kiwonsa a yankin Shen dake Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.
Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 12:30 na ranar Litinin, inda aka kuma kashe masa shanu uku da wasu tumakai.
Shugaban Ƙungiyar Ci-gaban Al’ummar Fulani ta GAFDAN, Garba Abdullahi da Shugaban ƙungiyar haɗaka ta ƙungiyoyin Fulani sun tabbatar da aukuwar lamarin.
Garba Abdullahi ya ce, an farmaki Sulaiman ne a lokacin ya ke tare da wasu makiyaya biyar.
Wani kawun mamacin mai suna Jafar Jibrin Bayero, ya yi alla-wadai da faruwar al’amarin, wanda ya bayyana yadda sauran makiyayan da suka tsira suka sanar da su cikin gaggawa.
Lamarin da ya sa suka hanzarta zuwa wajen sojoji a yankin Latiya tare da tafiya zuwa wajen da abin ya faru da wasu jami’ai.
Jagororin ƙungiyoyin Fulanin sun nemi hukuma da ta gudanar da bincike tare da kamo waɗanda ke da hannu a laifin tare da yin kira ga mabiyansu da su kwantar da hankula da kauce wa ɗaukar doka a hannu.
Jami’in hulɗa da jama’a na jami’an kula da ɓangaren kai ɗaukin gaggawa (EWER), Isa Abubakar, ya tabbatar da faruwar al’amarin, ya na mai cewa tuni suka sanar da hukumomin da ke da alhakin kula da lamarin don ɗaukar mataki a kai.
