Daga WAKILINMU
Mahukuntan gagarumin taron HIBAF na shekarar 2025, sun sanar da watan Yuni a matsayin watan da za a gudanar da taron a karo biyar, mai taken ‘Rumbunan Ilimi’.
Kamar yadda sanarwar da suka fitar ta bayyana, “Wannan biki zai zama wata kafa ce ta binciko da ƙarin fahimta game da samuwar rumbunan ilimin Hausawa kowane iri, taƙaitattu ko masu zurfi, waɗanda ke tafe da labarin asalin al’ummar Hausawa, tare da nazarin yadda tsarin ilimin Hausawa na gargajiya ya samo asali da ci gaba da gudana a tsawon zamani. Muhimmin batu a wannan bikin baje-koli shi ne amfanin da ke tattare da rumbunan ilimin Hausawa, wanda ya samo tushe daga adabin baka da hikimomin Hausawa da addinai da yanayin zamantakewa da ke wakana daga zamani zuwa wani zamani. Rumbunan ilimin gargajiya da Hausawa suka wanzu da su, suna nuna fahimtar al’ummar Hausawa game da hangen da suke yi wa duniya da abin da ke cikinta, wanda ya ƙunshi falsafar rayuwa da shugabanci da ɗabi’u da alaƙar al’ummar da da muhallinsu.
Zuwan Larabawa da addinin Musulunci a ƙasar Hausa ya kawo sabon salo ga tsarin samar da ilimi ga Hausawa, wanda ake iya gani ta hanyar amfani da rubutun Ajami—wato rubutun Larabci da aka daidaita domin rubuta Hausa da wasu harsunan Afirka. Rubutun Ajami ya zama wata muhimmiyar hanya wajen adana ilimin Hausawa na gargajiya da na addini da waƙoƙi da tarihi da kasuwanci. Wannan tsari shi ya haifar da auratauya tsakanin tsarin ilimin gargajiya da na Musulunci cikin wani salo da ya faɗaɗa rumbun ilimi da al’adu. Daga baya, shigowar ‘yan mulkin mallaka, wato Turawan Birtaniya da assasa tsarin ilimin mulkin mallaka da shigar da ilimin Boko ya kasance wata sabuwar hanya ta shata sabon tsarin ilimi, wanda ya saɓa wa tsarin gargajiya amma kuma ya kawo waɗansu damarmaki na tattaunawa da haɗin kai tsakanin baƙi da ‘yan gida a cikin ƙasar Hausa.
Duk da tsawon lokaci da aka ɗauka ana ganin wannan haɗaka, muhimmancin waɗannan rumbunan ilimi na da, da na yanzu suna nan daram. Da kuma aka shiga tsarin zamanantakewar zamani ta dijital da yadda ake samar da ilimi da sarrafa da adana da watsa shi a doron ƙasa da yadda yake sauyawa da canza kamanni, inda tsarin ilimin gargajiya; da ya ƙunshi tarihin baka da rubutun Ajami da adabin gargajiya suka kasance sahun gaba wajen sake dawo da martabar tsarin ilimin Hausawa, sai abin ya kasance mai burgewa. Adana abubuwan tarihi ta hanyar kafafen dijital da dandamalin bayar da labarai na baka da sababbin hanyoyin fassara da kayan tarihi suna tabbatar da cewa muryoyin al’ummar Hausawa da hikimominsu na tsawon tarihi suna cigaba da yin tasiri, ga kuma sababbin tsare-tsare da suke ƙarfafa ƙara fahimtar al’adun Hausawa da juriyar al’umma ta fuskokin rumbunan ilimi da ke wanzuwa a yau.
Bikin Baje Kolin Littattafai da Fasahohin Hausa, karo na 5, (HIBAF 2025), zai gudana ne ta hanyar tattaunawar ga-mu-ga-ku da ta haɗuwa ta-ka da gabatar da wasanni da raye-raye ba baje al’adun gargajiya da waƙoƙin baka da rubutattu da fassara da zane-zanen fasaha domin ƙwaƙulo irin yadda Rumbunan Ilimin Hausawa ke taka rawa wajen ciyar da harkokin adabi da fasahohin al’ummar Hausawa gaba a doron ƙasa.
Wannan bikin baje-koli, #HIBAF25 na buƙatar mahalarta da su natsu su yi tudabbari da yin dogon tataccen tunani game da tsarin Rumbunan Ilimin Hausawa da muhimmancin su wajen warware matsalolin yau da kuma gobe. Ta hanyar danganta al’amurran jiya da na zamananci, bikin na neman jaddada yadda ilimin gargajiya ya kasance tushen da ba ya gushewa don bayyana al’adu da haɓaka tunani da gudanar da tattaunawa a tsakanin al’umma.”
