Kano: An jinkirta tashin jirage yayin da ma’aikatan NiMET ke tawayen rashin biyan mafi ƙarancin albashi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ma’aikatan Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMET) a Jihar Kano, sun gudanar da zanga-zangar tawayen ƙin biyan su albashi da sabon tsarin mafi ƙarancinsa, lamarin da ya sabbaba jinkiri ga jirage masu sauka da tashi a Filin Jiragen sama na Malam Aminu Kano dake jihar.

Timothy Meshelia, wanda shi ne shugaban ƙungiyar haɗaka ta haɗin kan al’umma a shiyyar Arewa ta Yamma ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.

Ya zargi hukumar gudanarwa ta NiMET da cewa ta gaza fara biyan ma’aikatan da mafi ƙarancin albashi na N30,000 da N70,000 da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar a shekarar 2024.

Haka kuma, ba ta biyan su kuɗaɗen alawus ba da ƙin gudanar da wasu shirye-shirye gami da rashin biyan su kuɗaɗen da suke bi bashi da dai sauransu.

Ƙungiyar ta bai wa hukumar wata guda domin aiwatar da tsare-tsaren da aka gabatar mata a madadin ma’aikatan da wasu yarjejeniyoyi da aka yi da ita.

By Babaji