
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta ayyan Filin Jiragen sama na Bola Ahmed Tinubu dake Minna a Jihar Neja a matsayin na biyu ga Filin Nnamdi Azikwe dake birnin tarayya Abuja.
Ministan Sufurin Jiragen sama, Festus Keyamo ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da fara aikin jiragen Kamfanin Overland Airways a babban Filin na Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce, filin jiragen ya na da kayan aiki na zamani da da iya gogayya da kowane filin jirgin sama a duniya.
Saboda haka ne ya bayyana wa al’umma da hukumomin NCA da FAAN kan mayar da filin a matsayin zaɓi na biyu bayan na Abuja ga masu fita da shiga Nijeriya ta jiragen sama.
