Hajjin bana: Jihohi sun amince da 9 ga Mayu zuwa 2 ga Yuli a matsayin ranakun farawa da gama ɗaukar maniyyata

Spread the love

Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta bayyana cewa za a fara jigilar Alhazai zuwa ƙasa mai tsarki a ranar 9 ga watan Mayu, 2025, inda za a fara da birnin Madina. Wannan bayani ya fito ne bayan wata ganawa da hukumar ta yi da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, a fadar shugaban ƙasa. Kwamishinan ayyuka na NAHCON, Prince Anofi Elegushi, ya ce an tanadi dukkan abubuwan da ake buƙata a Makka da Madina, ciki har da masauki, abinci da sauran shirye-shirye domin tabbatar da nasarar aikin hajji ga alhazan Najeriya sama da 40,000.

A yayin wata ganawa daban da shugabannin hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi da wakilan kamfanonin jiragen sama, an tattauna yadda shirin ke tafiya. FlyNas za ta ɗauki alhazai 12,506 daga jihohin Legas, Kebbi, Zamfara da sauransu, yayin da Max Air zai ɗauki 15,203 daga Kano, Katsina, Kwara da wasu. Kamfanin Umza zai ɗauki 10,163 daga Kaduna, Adamawa da Yobe, yayin da Air Peace zai ɗauki 5,128 daga jihohin Kudu maso Gabas da wasu. Dukkan jiragen za su kammala jigilar zuwa Saudiya kafin 24 ga Mayu, sannan a fara dawo da Alhazai daga 13 ga Yuni zuwa 2 ga Yuli.

A wani ɓangare na shirin, hukumar jin daɗin alhazai ta Jihar Kano ta fara rabon kayayyakin aikin hajji ga alhazanta. Daraktan hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Ɗanbappa, ya buƙaci alhazai su nemi kayansu daga ofisoshin ƙaramar hukuma, tare da jan kunne kan kawo kaya da ba su dace ba. Kayayyakin da aka raba sun haɗa da jakunkuna, hijabai, kayan maza da mata, da kuma jakunkunan da za a zuba kuɗi da takardu masu muhimmanci. Shugaban hukumar, Alhaji Yusuf Lawan, ya buƙaci alhazai su yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata.

By ukarofi